26 Yuli 2021 - 16:48
An Tsaurara Matakai A Filayen Jirgin Saman Tunusiya Don Hana ‘Yan Majalisa Ficewa Daga Кasar

Rahotanni da suke fitowa daga ƙasar Tunusiya suna nuni da cewa an tsaurara matakan tsaro da sanya ido sosai a filayen jiragen saman ƙasar a yau din nan Litinin a ƙoƙarin da ake yi na hana ‘yan majalisar ƙasar da aka dakatar da aikinta ficewa daga ƙasar zuwa waje.

ABNA24 : Rahotannin sun ce tun da safiyar yau Litinin aka tsaurara matakan sanya ido kan dukkanin filayen jiragen saman ƙasar Tunusiyan don haka ‘yan majalisar ƙasar da kuma duk wani wanda aka aike masa da sammaci ficewa da kuma gudu daga ƙasar.

Wannan matakin dai yana zuwa ne bayan da shugaban ƙasar Tunusiyan Kais Saied ya sanar da korar firayi ministan ƙasar Hicham Mechichi da kuma dakatar da ayyukan majalisa.

Shugaba Kais Saied ya dau wannan matakin ne biyo bayan rikici da munanan zanga-zangogin da suka faru a wasu biranen ƙasar saboda yadda gwamnatin take mu’amala da batun cutar nan ta COVID-19 da kuma tattalin arzikin ƙasar, lamarin da ya sanya wasu daga cikin masu zanga-zangar kai hari cibiyoyi da ofisoshin jam’iyyar Ennahdha babbar jam’iyya a majalisar ƙasar.

Har ila yau shugaban ya sanar da ɗage rigar kariyar da ‘yan majalisar suke da ita daga gurfanar da su a gaban kotu. Akwai dai wasu daga cikin ‘yan majalisar da wasu jami’ai da ‘yan siyasa da ake zargi da aikata wasu laifuffuka da suka haɗa da almundahana da sauransu da ake ganin cire musu wannan riga ta kariya za ta iya shafarsu.

342/